Save Arewa Poem by Abdulrauf Muhammad Aljasawee

Save Arewa

Rating: 1.0

•Da sunanka gwani na zana fara
•Ka ban hikima ni zana rera
•Waƙar ƴanci na taho na tsara
•Cikin hikima da farar dabara
•Nayo baitoci na da rana,

•A yau a ƙasar mu fa babu ƴanci
•Babu tsaro dan bamu bacci
•babu sukunin cin abinci
•A kashe mu cikin ƙauye a arce
•A birnin ma dai babu tsira,

•ga ƙazantar fyaɗe duk ana yi
•ƴan mata sun zam babu ƴanci
•babu tsaro kuma ba aminci
•gaskiyar shari'a kuma tai ƙaranci
•ta zamo cinikayyar kasuwanci
•ya ƙawiyyu ka tarwatsa masu ɓarna,

•Muna fama da rashin tsaro ma
•A zamfara sokkoto har Kano ma
•Da brono kaduna da yobe nan ma
•Katsinan dikkon ma babu dama
•Ya Jalla ka taimaki ƴan Arewa,

•shugabacin ƙasar nan duk fa mune
•shugaban sojoji namu nan ne
•shugaban ƴan sandan ma fa mune
•madafun ikon duk fa mune
•sannan mu adda rshin tsaro ma,

•garkuwa da mutane har a fili
•balle lungu inda babu sarari
•a karɓi kudin fansa da tsauri
•a barmu cikin firgici da rauni
•mu aminci munka bida Arewa,

•ya ilahu ina roƙo Wahabu
•ka rusa shirin duk masu ƙin mu
•ka isar mana ba wayo garemu
•ka tsare mu da sharrin dukka mugu
•ka yaye matsalar ƴan Arewa.

©✍️ Abdulrauf Muhammad Aljasawee 🇳🇬
29/01/2021

Save Arewa
POET'S NOTES ABOUT THE POEM
This poem is written in a popularly known african language called Hausa, the native tongue of the poet, but it will soon be translated in english for a better understanding.
COMMENTS OF THE POEM
READ THIS POEM IN OTHER LANGUAGES
Close
Error Success