Mafarkin Kogin Fura 2 Poem by Garba Ado Ibrahim

Garba Ado Ibrahim

Garba Ado Ibrahim

follow poet
Garba Ado Ibrahim
follow poet

Mafarkin Kogin Fura 2

Tsamiyar ta ja'ira kura,
Kogin fura ga sahibi gurin fura?
Na aminta amma acikin batun,
Ka tausayawa hattara,
Hakane abban Humaira!
Hakane abban Humaira!
Hakane abban Humaira!
Ko ina hayaniya da kaudi'
Ga ka'ra,

Asaurara! Asaurara!
Asaurara!
Dan Allah ayi haku'ri asaurara,
ka ji aikin manya zagi,
Agun mai kogin fura,
Kar a tura yallabai' mak'ku'ra,
Ku gane rai ya dade' ba ya son ka'ra,
Saboda ku ya tsaya acikin ku'ra,
Amakon jiya kan lafiya,
Ya dawo daga missira,

Ba zancen faskara,
Bayan kogin fura,
Za a jawo tekun fura,

Akai kuma jirgin ruwa zai saffara?
Muryar da gano mai ita,
Sai da ya faskara,
Acikin masu sauraren kogin fura,
Ina ruwanka da jirgin ruwa,
In ka kere fura?
Amsar jagoran tono kogin fura,
Ni dai ku taimaka in wafto takara,
Za ku warke da siyan fura,

Anya ba bu batun damfara?
Wani mai tambaya gashi ga furfura,
Ayau ina da shekarun da,
Sun sha kan shatara,
Ina jin labaran gida,
Har in ka ke'tara,
Birtaniya, ko Amurka Jamus,
Duk in ka tattara,
Kimiyyar duniya,
Sun zarce dan'kira.

Monday, November 26, 2018
Topic(s) of this poem: nature
COMMENTS OF THE POEM
Be the first one to comment on this poem!
READ THIS POEM IN OTHER LANGUAGES
Garba Ado Ibrahim

Garba Ado Ibrahim

follow poet
Garba Ado Ibrahim
follow poet
Close
Error Success